fidelitybank

Sojoji sun gano Naira miliyan 60 da za a miƙawa ƴan ta’adda

Date:

Rundunar soji ta ce, dakarunta sun gano Naira miliyan 60 da aka yi nufin kai wa ‘yan ta’adda kudin fansar karbo wasu daga cikin wadanda ‘yan bindiga suka yi garkuwa da su.

Jaridar PRNigeria da ke da alaka da jami’an tsaron Najeriya ta rawaito cewa sojin sun ce ana zargi a cikin wadanda aka samu da kai kudin fansar har da jami’an tsaron farin-kaya wato DSS.

Har wa yau, dakarun sun yi nasarar kubutar da wasu mutane da aka yi garkuwa da su da suka hada da mata da kananan yara.

Dakarun, wadanda suka hada da sojin sama da na kasa, sun kai ga cin karfin ‘yan bindigar. An gano muggan makamai da bindiga kirar AK47, da albarusai da sauransu.

Sojojin sun ce za su mika batun jami’an tsaron da suka hada da na DSS da ake zargi da kai kudin fansar ga ma’aikatar tsaron Najeriya, domin gudanar da bincike

sahara hausa

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

IGP ya ba da umarnin bincike kan bidiyon ƙorafin wani tsohon ɗansanda

Babban Sufetan ‘Yan Sandan Najeriya, Kayode Adeolu Egbetokun, ya...

Amurka za ta bayar da gudunmawar dala miliyan 30 ga ‘yan Gaza

Amurka za ta ba da tallafin dala miliyan talatin...

Iran na binciken ɓarnar da aka yi cibiyoyin nukiliyar ƙasar

Ministan harkokin waje na Iran ya amince an yi...

Japan ta zartar da hukuncin kisa a karo na farko

Japan ta zartar da hukuncin kisa a karon farko...

Sojoji na zaman makoki na kwanaki 3 bayan an kashe Jami’ai 17

Rundunar Sojin sama ta bayyana fara zaman makoki na...

‘Yan Ta’adda ba za su samu mafaka ba a Nasarawa ba – Gwamna

Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule ya musanta zargin da...

Sojoji sun mayar da martani kan ‘Yan ta’addan Neja

Dakarun Sojin Saman kasar nan, sun ce sun ƙaddamar...

Kotu ta yanke wa Matashin da ya kashe Budurwarsa hukuncin kisa

Kotun babban birnin jihar Nasarawa ta yanke wa wannan...

PDP ta yi watsi da matakin shugaban jam’iyyar da ya dauka

Kwamitin amintattu na jam’iyyar PDP, ya yi watsi da...

Tinubu zai sanya hannu kan sabbin dokokin haraji

Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, zai sanya hannu kan...

‘Yan Bindiga sun kashe Sojoji a Neja

Rundunar Sojin Kasa, ta tabbatar da mutuwar wasu daga...

Kungiyoyi 110 suna bukatar mu yi musu rijista – INEC

Hukumar zaɓen Najeriya, INEC ta tabbatar da samun buƙatu...
X whatsapp