Rundunar sojin Najeriya a ranar Alhamis ta ce, dakarunta da aka tura domin tunkarar ‘yan tada kayar baya a yankin Arewa maso Yamma, sun yi nasarar kare kauyen Damba Dikko, al’ummar karamar hukumar Illela a jihar Sokoto, daga harin da ‘yan tada kayar baya suka kai musu na neman karbar haraji daga hannun mutanen kauyen.
Daraktan hulda da jama’a na rundunar, Manjo Janar Onyema Nwachukwu ne ya bayyana hakan.
Onyema ya ce, dakarun ‘yan banga sun yi gaggawar afkawa kauyen inda suka yi artabu da ‘yan ta’addan tare da kashe biyu daga cikinsu tare da kubutar da wasu mutanen kauyen biyu da aka yi garkuwa da su.
Ya bayyana cewa mutanen kauyen da aka ceto wadanda suka samu kananan raunuka sun samu kulawar likitoci daga hukumar kula da lafiya ta NA.
“A wannan rana, sojojin Najeriya a cikin wani gagarumin aikin ceto, sun zakulo wasu mutane hudu da wasu gungun masu garkuwa da mutane suka yi garkuwa da su a jihar Edo.
“Masu garkuwa da mutanen sun yi garkuwa da su da karfin tsiya, wadanda suka hada da wata mata da wasu mutane uku cikin dajin Ososo da ke karamar hukumar Akoko Edo a jihar, amma sai gaggan sojojin suka bi su, suka kama su, inda suka yi ta harbe-harbe tare da zakulo wadanda suka yi garkuwa da su.
“Sojojin sun kama daya daga cikin masu garkuwa da mutane, wanda a halin yanzu ana gudanar da bincike na share fage, daga nan kuma za a mika shi ga hukumar da ta dace. Daya daga cikin wadanda aka ceto wadanda suka gamu da firgici da kasala, an kwashe su zuwa asibiti, inda yake karbar magani, yayin da wasu kuma aka mika su ga iyalansu,” inji Onyema.
Kakakin rundunar ya ce rundunar ta yabawa jama’a bisa hadin kan da suke baiwa sojoji da sauran jami’an tsaro wajen yaki da kalubalen tsaro a kasar.
Ya kuma kara musu kwarin guiwa da su ci gaba da taka tsan-tsan tare da gaggauta kai rahoton duk wani yunkuri da ake zargin an yi na karya tsaro ga hukumomin da abin ya shafa.