fidelitybank

Sojoji sun farwa ‘yan IPOB a jihar Delta

Date:

Rundunar Sojin Najeriya, a ranar Asabar din da ta gabata, ta ce dakarun da ke karkashin runduna ta 6, sun lalata wani yanki na haramtacciyar kungiyar ‘yan asalin yankin Biafra, IPOB/Eastern Security Network, ESN, a garin Asaba na jihar Delta.

Daraktan hulda da jama’a na rundunar, Birgediya Janar Onyema Nwachukwu, ya ce farmakin da suka kai a ranar Asabar ya kai ga yin musayar wuta, lamarin da ya tilasta musu barin maboyarsu cikin rudani.

A sanarwar ya ce sojojin sun kama daya daga cikin mayakan da suka tsere tare da kwato bindigu kirar AK-47 guda biyar, Pump Action Semi Automatic rifles guda uku, bindiga G3 daya da kuma bindigar ganga guda daya.

Sauran kayayyakin da aka kwato sun hada da harsashi masu rai, injin lantarki, adduna, gatari da tutar kungiyar IPOB.

A cewarsa, sojojin sun lalata yankin tare da yin amfani da dajin wajen fatattakar mayakan da suka tsere.

Ya ce babban hafsan sojin kasa, Manjo Janar Taoreed Lagbaja ya yabawa sojojin da sauran jami’an tsaro bisa kokarin da suke yi a ayyukan da suke ci gaba da yi, ya kuma bukace su da su ci gaba da dagewa don dawo da hayyacinsu a yankin.

besda

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp