Rundunar sojan Najeriya ta ce ta yi wa mayaƙan ƙungiyoyin Boko Haram na ISWAP kwanton ɓauna a yankin Mallumti na jihar Borno.
Wata sanarwa da ta fitar da yammacin Lahadi, rundunar ta ce, Bataliya ta 109 ce da ke Magumeri ta gudanar da samamen, inda ta shiga sansanin ‘yan bindigar.
Ta ƙara da cewa, dakarun nata sun kashe ‘yan ƙungiyar da dama tare da ƙwato makamai da ababen hawa.
Sauran abubuwan da ta ƙwato sun haɗa da wayoyin salula da kayayyakin haɗa abubuwan fashewa. Ta ce har ya zuwa lokacin da ta fitar da sanarwar tana ci gaba da aikin sintirin.