Rundunar sojiji ta ce, sojoji tare da haɗin gwiwar ƴan sa-kai waɗanda ake kira Bijilanti sun samu nasara a wata fafatawa da su ka yi da ƴan bindiga a ƙauyen Warari da ke Jihar Neja.
Rundunar ta ce a lokacin artabun, wadda ta faru a jiya Talata ta kashe fiye da ‘yan bindiga 100 waɗanda ke gilmawa a kan babura.
Lamarin ya faru ne bayan da sojojin suka samu sahihan bayanai daga mazauna yankin game da hanyoyin da ‘yan bindiga ke bi don satar shanu.
Wannan ne ya bai wa sojojin damar kitsa kwanton-ɓauna da ya kai ga fafatawar da ta kai ga hallaka ƴan bindigan da dama.
Jaridar PRNigeria ta ambato shaidun da suka ce sojojin sun yi amfani da motoci masu sulke da makamai na zamani wanda ya ba su galaba a kan ‘yan bindigar.
Shugabannin al’umma a Warari sun tabbatar da girman rashin da ‘yan bindigar suka tafka, inda suka bayyana cewa gawarwakin wasu daga cikin su sun bazu a tituna da gonaki da dazuka da ke kewaye da yankin.
Neja na cikin jihohin Najeriya da ke fama da hare-haren ƴan bindiga masu kisa da kuma garkuwa da mutane domin neman kudin fansa.