Dakarun rundunar hadin gwiwa ta Multinational Joint Task Force (MNJTF) mai suna ‘Operation Hadin Kai, Sector 3’, sun dakile wani yunkurin kai hari da ‘yan ta’addar ISWAP suka yi a yankin Magumeri-Maiduguri a Borno.
Sojojin sun kuma kwato tarin alburusai daga hannun ‘yan ta’addan a wani farmaki da suka kai musu na dabara a yankin.
Lt.-Kol. Olaniyi Osaba, babban jami’in yada labarai na soji, MNJTF, N’djamena, Chadi, ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi a Maiduguri.
Ya ce sojojin sun aiwatar da wani harin kwanton bauna, inda suka kawar da barazanar kafin ‘yan ta’adda su yi barna a kan fararen hula da ba su ji ba ba su gani ba.
Osaba ya ce sojojin sun ajiye kansu cikin dabara a kan hanyar ‘yan ta’addan inda suka yi ta artabu da su a lokacin da suka fito daga wani daji a kan babura.
“Da ganin sojojin, ‘yan ta’addan sun yi yunkurin guduwa amma sun ci karo da manyan bindigogi.
“Wannan gagarumin aiki ya tilasta musu barin makamansu da babura, wanda hakan ya kawo cikas ga shirinsu na tayar da rikici a yankin,” in ji shi.
Ya lissafta makaman da aka kwato sun hada da Bindigu AK-47 guda biyu, harsashi na musamman 7.62mm 51, mujallu guda biyu, harsashai 61 na 7.62 na NATO, buhunan tabar wiwi da Tramadol da dai sauransu.