fidelitybank

Sojoji sun daƙile harin Boko Haram a Borno

Date:

Rundunar sojin kasar nan ta ce, sojojinta na Operation Hadin Kai sun yi nasarar daƙile wani hari da ‘yan Boko Haram da /ISWAP suka kai da tsakar dare a garin Marte ta Jihar Borno.

Harin wanda ya fara da misalin karfe 1:35 na daren ranar Litinin, ya janyo arangama mai zafi tsakanin sojojin Najeriya da ƴan Boko Haram ɗin inda sojojin suka kashe da dama daga cikin su.

Rundunar sojin ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na X.

Rundunar ta kuma tabbatar da mutuwar sojoji biyu a yayin faɗan, yayin da sojojin suka ci gaba da bin sahun masu ƴan Boko Haram ɗin da suka tsere.

Garin Marte dai na daga cikin wuraren da Boko Haram ke yawan kai hari saboda matsayinsa na tasha da hanyar shiga garuruwa

Gwamnan Jihar, Babagana Umara Zulum, ya taba yin kira ga gwamnatin tarayya da ta ƙara azama wajen ƙarfafa ayyukan tsaro a garin Marte da kuma kare garin da komawa hannu ƴan Boko Haram.

Harin da aka kai na ranar Litinin ya sake tunatar da yadda Boko Haram ke ci gaba da zama barazana ga ƴan Najeriya.

daily sun news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp