fidelitybank

Sojoji sun ceto ƴan Chibok 3 bayan artabu da ƴan Boko Haram

Date:

Rundunar sojin hadin-gwiwa ta ‘operation Hadinkai’, ta ce, ta murkushe wasu ‘yan ta’adda 60, da kuma cafke mutum 120 da ake zargin ‘yan ta’adda ne a wani samame da suka kai a kauyukan jihar Borno.

Rundunar ta kuma ce, ta yi nasarar sake ceto wasu ‘yan matan Chibok uku da Boko Haram ta sace daga makarantar Sakandaren mata ta Chibok, a Borno tun 2014. In ji BBC.

Kwamandan rundunar, Manjo Janar Christopher Musa, da ke yi wa ‘yan jarida karin haske kan ayyukansu a hedikwatarsu da ke Maiduguri, ya ce jami’ansu na ci gaba da kokarin da katse duk wata hanya da mayaƙan ke samun taimako da makamai.

Sannan suna samun nasarar cafke mutanen da ke aiki da mayaƙan wajen kai musu abinci da sauran kayayyakin amfani.

‘Yan matan da aka ceto, tsakanin 27 ga watan Yuni zuwa 25 ga watan Yuli, sun hada da Ruth Bitrus, Karuna Luka da ke dauke da jariri sai kuma Hannatu Musa mai yara biyu.

A Afrilun shekara ta 2014 ne dai mayakan Boko Haram suka yi garkuwa da ‘yan mata 276 daga sakandaren kwana ta Chibok, galibinsu a wannan lokaci shekarunsu na tsakanin 16 zuwa 18.

today daily post news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Kare Ya Kashe Ragon Layya: Mai ƙwacen waya ya kashe Sojin ruwa a Kaduna

Wani mai ƙwacen waya ya kashe wani soja bayan...

Sojoji sun hallaka ƴan Boko Haram da dama

Da sanyin safiyar ranar Litinin, dakarun rundunar Haɗin kai...

Tarzomar kama baƙin haure a Amurka na yamutsa hazo

An shiga rana ta uku a tarzomar da ake...

Alhazai sun kammala aikin Hajji bana

A ranar Lahadin da ta gabata ne alhazai miliyan...

Tinubu gyaran ƙasa za ka mayar da kai ba zaɓen 2027 ba – ACF

Ƙungiyar Tuntuɓar Juna ta Arewacin Najeriya, ta yi kira...

Ƴan Jagaliya sun caka wa Matashi kuwa lokacin da ya zo karɓar naman Sallah a Kano

Matashi Ibrahim Mahmud ya rasu sakamakon caka masa wuƙa...

Kallo Ya Koma Sama: Elon Musk zai fuskanci mummunar sakamako – Trump

Ana ci gaba da takun saka tsakanin shugaban Amurka...

Zulum ya miƙa kyautar Naira miliyan 100 ga iyalan Sojojin da aka kashe

Gwamna Babagana Umara Zulum na jihar Borno, ya bai...

Otal ɗin ƴan Najeriya ya kama da wuta wani ɓangaren a Saudiyya

Hukumar Alhazai ta Najeriya ta ce an samu tashin...

An kai hari maɓoyar Boko Haram a Borno

Biyo bayan sahihan bayanan sirri da aka samu, rundunar...

Alaƙar Trump da Elon Musk ta yi tsami sosai

Attajirin da ya fi kowa arziki a duniya, Elon...

An yi jana’izar Muhammad Uwais

An gudanar da jana'izar tsohon alkalin alkalan Najeriya, mai...
X whatsapp