Dakarun Sojojin Najeriya na Brigade 21 masu sulke a karamar hukumar Bama, sun ceto wasu ‘yan mata biyu da ‘yan ta’addan Boko Haram suka yi garkuwa da su a Sakandaren ’yan mata na gwamnati da ke garin Chibok a Jihar Borno a shekarar 2014.
‘Yan matan biyu, Hannatu Musa da Kauna Luka, an ceto su ne a ranar Talata, 26 ga watan Yuli, shekaru takwas bayan sace su.
Kungiyar Boko Haram, ta yi garkuwa da dalibai mata 276, masu shekaru tsakanin 16 zuwa 18 a makarantar Sakandaren ’yan mata ta gwamnati da ke garin Chibok a ranar 14 ga Afrilu, 2014.
A cewar wani rahoton sirri da aka samu daga manyan majiyoyin soji na Zagazola Makama, kwararre kan yaki da tada kayar baya kuma mai sharhi kan harkokin tsaro a tafkin Chadi, ‘yan matan sun tsere daga sansanin Gazuwa, hedikwatar kungiyar Jama’at Ahl as-Sunnah lid-Da’wah. wa’l-Jihad, bangaren Boko Haram, wanda a da ake kira Gabchari, Mantari da Mallum Masari, da ke da nisan kilomita tara zuwa garin Bama.
Tun da farko dai, wasu ‘yan matan makarantar Chibok da aka ceto, Mary Dauda da Hauwa Joseph, sun shaida wa hukumomin soji cewa akwai ‘yan matan makarantar Chibok kusan 20 da har yanzu ake tsare da su kuma aka yi musu auren dole a sansanin Gazuwa.