Dakarun runduna ta daya ta Najeriya, sun ceto wasu mutane hudu da aka yi garkuwa da su a sansanin ‘yan ta’adda da ke karamar hukumar Kajuru a jihar Kaduna.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mukaddashin mataimakin daraktan hulda da jama’a na rundunar sojan Najeriya ta daya, Laftanar Kanar Musa Yahaya ya fitar.
A cewar sanarwar, sojojin a yayin da suke aiki da sahihan bayanan sirri, sun kai wani gagarumin farmaki a Kajuru.
Ya ce a yayin farmakin sojojin sun yi arangama da ‘yan bindiga/ masu garkuwa da mutane inda suka yi musu artabu da bindiga, lamarin da ya tilasta musu yin watsi da wadanda abin ya shafa tare da kai musu dauki da raunuka daban-daban.