fidelitybank

Sojoji sun ceto mutane 40 daga hannun ‘yan bindiga a Zamfara

Date:

Dakarun soji sun ce, sun ceto mutum 40 da ƴan bindiga suka garkuwa da su a jihar Zamfara.

Dakarun da ke aiki ƙarƙashin rundunar Operation Hadarin Daji sun samu nasarar ceto mutanen ne a karamar hukumar Bukkuyum na jihar.

Gidan talabijin na Channels ya ruwaito cewa sojojin sun samu nasarar ce bayan samun bayanan sirri da ke cewa ƴan bindigar sun yi garkuwa da mutanen da ba a san adadinsu ba a ƙauyen Kyairu da Alkama da ke karamar hukumar ta Bukkuyum.

Bayan nan ne sojojin suka tasamma garin da nufin kai samame domin ƙwato mutanen da ke hannun ƴan bindigar a ranar Talata.

Sai dai sojojin sun yi bata kashi da ƴan bindigar na wasu sa’o’i kafin su fi karfinsu da tilasta musu tserewa da kuma barin mutanen da suka yi garkuwa da su.

Mutanen da aka ceto ɗin da suka kai 40 tuni suka haɗu da iyalansu yayin da aka miƙa goma daga cikinsu kuma ga hannun Sarkin Gwashi domin haɗa su da iyalansu.

nnn news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp