Rundunar Sojin Najeriya ta bayyana cewa, dakarun Brigade 17, na sojojin Najeriya tare da hadin gwiwar ‘yan sandan Najeriya, sun ceto wasu jami’an masu yiwa kasa hidima guda biyu da wasu ‘yan bindiga suka yi garkuwa da su a unguwar Yargoje da ke karamar hukumar Kankara a jihar Katsina.
Daraktan hulda da jama’a na rundunar, Birgediya Janar Onyema Nwachukwu ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a.
Nwachukwu ya sanar da cewa, ‘yan ta’addan sun yi awon gaba da jami’an hukumar ne a lokacin da suke kan hanyar wucewa daga Edo zuwa jihar Katsina, inda ya kara da cewa, daukin gaggawar da jami’an soji da ‘yan sanda suka yi ne ya yi nasarar kubutar da wadanda abin ya shafa daga hannun wadanda suka yi garkuwa da su.
Ya ce an bai wa ‘yan kungiyar da aka ceto damar kula da lafiyarsu tare da tallafa musu domin tabbatar da lafiyarsu da ta jiki kuma a halin yanzu suna hannun ‘yan sandan Najeriya da ke Kankara.
Rundunar ta kuma nemi hadin kan jama’a da goyon bayan jama’a wajen samar da bayanan da suka dace don inganta ayyukan rundunar da suke yi na tunkarar wasu miyagun da ke barazana ga tsaron kasa.