Dakarun Operation Hadin Kai, sun yi nasarar kubutar da wasu direbobin motocin wuta guda hudu da wasu da ake zargin ‘yan kungiyar IS ne a yankin yammacin Afirka (ISWAP) suka yi garkuwa da su.
An sace direbobin ne a ranar Asabar, 27 ga watan Mayu, kusa da kauyen Ngwom dake karamar hukumar Mafa. Mafa dai na da tazarar kilomita 50 daga gabas da Maiduguri babban birnin jihar Borno a arewa maso gabashin Najeriya.
Rahotanni sun bayyana cewa direbobin sun kai ’yan kwadago wadanda galibinsu masu yankan itace da lodi ne zuwa daji lokacin da ‘yan ta’adda dauke da makamai suka tare su.
‘Yan ta’addan sun tunkari direbobin ne da sunan cewa suna bukatar aikinsu domin kai mambobinsu wani kauye da ke kusa. Sai dai ba da jimawa ba ‘yan ta’addan suka yi garkuwa da direbobin da fasinjojinsu.
Majiyar leken asirin ta bayyana cewa bayan samun wannan kiran na gaggawar, sojojin 112 Task Force Battalion, Mafa, tare da Civilian JTF da mafarauta sun tashi daga Mafa suka nufi kauyen Gullo domin neman wadanda aka sace a ranar 1 ga watan Yuni, 2023.
Majiyar ta ce da ganin sojojin da suke fada, ‘yan ta’addan sun yi watsi da wadanda harin ya rutsa da su, suka gudu yayin da sojoji suka yi musu zazzafar kora.
Dakarun fadan sun yi nasarar ceto mutanen hudu da aka yi garkuwa da su tare da kwato motocin.


