Rundunar soji ta sanar a ranar Alhamis cewa, sojoji sun kama wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne da ke ba wa shugaban ‘yan bindiga, Bello Turji bindigu.
Rundunar sojin ba ta bayyana sunayen mutane ukun da aka kama a Kaduna ba tsakanin ranakun 14 zuwa 17 ga watan Nuwamba, 2023.
An bayyana Turji da wasu 18 a hedikwatar tsaro a ranar 14 ga Nuwamba, 2022, kuma an sanya musu kyautar Naira miliyan 95 a kawunansu.
Turji, wanda ake yi wa kallon daya daga cikin manyan ‘yan bindigar ‘yan fashi, ana zarginsa da hannu a mutuwar sama da mutane 200, ciki har da mata da yara, a watan Janairun 2022.
Ana kuma zarginsa da hannu a harin da aka kai kauyen Garki da ke Sokoto a shekarar 2021, inda aka kashe sama da mutane 80 a dare guda.
Turji ya kaucewa hare-haren sama da sojoji suka kai masa da nufin kashe shi a lokuta da dama.
Darakta mai kula da harkokin yada labarai na tsaro Manjo Janar Edward Buba ya shaidawa manema labarai a Abuja cewa wadanda ake zargin suna kan hanyarsu ta ba kwamandan ‘yan fashi da makami a Zamfara makamai da harsashi ne a lokacin da sojoji suka kama su.
Ya ce, “Tsakanin ranar 14 zuwa 17 ga watan Nuwamba, 2023, sojoji sun gudanar da wani samame daban-daban sun kama wasu da ake zargin masu sayar da makamai ne (an boye sunayensu) a kananan hukumomin Zango Kataf da Kagarko na jihar Kaduna.
“Bincike na farko ya nuna cewa suna kan hanyarsu ta kai wa Bello Turji alburusai, wanda fitaccen dan ta’adda ne a jihar Zamfara.
“Sojoji sun kwato 504 na 7.62mm Special ammo, 100 na 7.62mm NATO ammo, caja RPG guda uku, wayoyin hannu uku, katin ATM daya, da mota daya.”