fidelitybank

Sojoji sun bude wuta a kan ‘yan ta’addan Zamfara

Date:

Rundunar Operation Hadarin Daji ta samu nasarar kai hari mai zafi a kan sansani ‘yan bindiga da ke dajin Totsari da Kenkashi a karamar hukumar Tsafe cikin Jihar Zamfara.

Mazauna Mada ne suka sanar da manema labarai hakan a ranar Laraba, inda suka ce, lamarin ya auku ne yayin da sojojin suka kai samame kauyen Getawa, Unguwan Kade da kauyen Maigalma.

A cewar majiyar, yayin da ‘yan bindiga suka nemi tserewa daga sojoji, sun zubar da babura da shanu da suka sace, inda sojojin suka bisu suna ta harbin su.

Wani shaida da ya tabbatarwa da gidan talabijin na Channels ya ce, “Yayin da ‘yan bindigan suke kokarin tserewa daga rundunar sojojin sun bude musu wuta daga nan suka saki shanun satar suka fara gudu. Take anan sojojin suka bi su suna harbi. “Sakamakon samamen, an halaka dan ta’adda daya sannan an kwato babura da shanaye da dama da suka sace.” 

“Sojojin sun bincike sansanin tsaf inda suka lalata shi sannan yanzu haka sun mamaye kauyakun suna ci gaba da bincike ko ina.” 

nigerian 
news today

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp