fidelitybank

Sojoji sun aika Gwaska Dankarami da ‘yan Bindiga 100 lahira a Katsina

Date:

Hukumomi a kasar nan sun ce, jami’an tsaron ƙasar nan sun halaka ƴanbindiga 100 ciki har da gawurtaccen ɗanbindiga, Gwaska Dankarami a jihar Katsina.

Hadin gwiwar jami’an tsaron kasar ne suka ƙaddamar da harin a ranar Juma’a wanda ya yi sanadin kisan Gwaska Dankarami – wanda ya kasance mataimakin shugaban ƙungiya mai alaƙa da ISWAP.

Bayanai sun nuna cewa Gwaska Dankarami ya jima yana ɓuya a dajin Munumu da ke jihar Katsina.

Rahotonni sun ce sojojin sun lalata maɓoyar ƴanbindigar da dama a sassan jihar a lokacin harin, tare da ƙwato da kuma lalata wasu manyan bindigogi masu jigida da waɗanda aka ƙera a cikin gida.

Harin na zuwa ne bayan da a farkon mako ƴanbindigar suka yi garkuwa da mutum 43 mazauna ƙauyukan Maigora da ke yankin ƙaramar hukumar Dandume

Kwamishinan al’amuran cikin gida na jihar Katsina, Nasir Mu’azu ya bayyana matakin da wata gagarumar nasara a yaƙi da ƴanbindiga ake yi a jihar.

“Abin farin ciki ne ga jihar, domin wannan nasara ta taimaka wajen wargaza hadakar ƴanbindigar da ke addamar garuruwa da ƙauyukan yankunan ƙananan hukumomin Faskari da Kankara da Bakori da Malumfashi da kuma Kafur,” in ji Kwamishinan.

Ba dai wannan ne karon farko da jami’an tsaron Najeriya ke bayar da labarin kashe Gwaska Dankarami ba, ko a 2022 ma rundunar sojin sama ta ƙasar, ta yi iƙirarin kashe shi a irin wannan hari.

nnn hausa

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp