fidelitybank

Sojoji sun ƙaddamar da magance rikici a Filato mai taken Haƙorin Damisa

Date:

Babban hafsan sojin ƙasa na Najeriya, Manjo Janar Taoreed Lagbaja ya ƙaddamar da sabuwar rundunar soji mai suna ‘Haƙorin Damisa’ da za ta yi yaƙi da rikicin ƙabilanci da na tsakanin manoma da makiyaya a ƙaramar hukumar Mangu da ke jihar Plateau.

Cikin wani sakon Twitter da rundunar sojin ta wallafa, ta ce an ƙaddamar da rundunar ne domin magance tashe-tashen hankulan da ake yawan samu, a ƙaramar hukumar, lamarin da ke ƙara haifar da taɓarɓarewar tsaro a yankin.

Yayin da yake jawabi ga dakarun rundunar, a lokacin ƙaddamarwar, babban hafsan soji ƙasa na Najeriya, ya yi kira a gare su da sun kawar da duka wani nau’in barazanar tsaro da yankin ke fuskanta da ma jihar Plateau baki-ɗaya.

Manjo Janar Lagbaja ya ce dakarun su tabbatar sun yi duk mai yiwuwa domin tabbatar da tsaron lafiyar mazauna yankin, ta hanyar gaggauta kai ɗauki a duk inda aka buƙace su.

Ya kuma sake nanata wa sojojin irin ƙwarin gwiwar da al’umma gari ke da shi a kansu.

Haka kuma babban hafsan sojin ƙasar ya gana da masu ruwa-da-tsaki na ƙaramar hukumar, inda ya yi kira a gare su, da su nuna kishi wajen maido da zaman lafiya a ƙaramar hukumar, wani abu da ya kira ”Babban aikin maido da zaman lafiya a Mangu”.

Yana mai cewa babu wanda zai kai al’ummar garin tare da iyalansu jin daɗi, idan aka samu samu zaman lafiya a yankin.

A baya-bayan nan dai an samu rahotonnin tashe-tashen hankula a garin na Mangu.

Jihar Plateau na daga cikin jihohin Najeriya da ke yawan fama da rikice-rikice masu alaƙa da addini da ƙabilanci da na manoma da makiyaya.

sun newspaper nigeria

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp