‘Yan majalisa a Mali sun amince baki ɗayansu da wani shirin gwamnatin sojan ƙasar da ke son ci gaba da zama a mulki har tsawon shekara biyar nan gaba.
Har yanzu ba a bayyana ranar da za a gudanar da zaɓe ba a ƙasar.
A shekarar da ta gabata ya kamata a gudanar da zaɓen amma sai ba a yi ba, abin da ya sa ƙungiyar Ecowas ta sanya mata takunkumai.
Yanzu Mali na bin hanyoyin shari’a don a ɗage mata takunkumin da ƙungiyar harkokin kuɗi ta Afirka ta Yamma, Uemoa, ta sanya mata yayin da take fama da bashi. In ji BBC.