Jami’an tsaro na ci gaba da neman fiye da dalibai 280 na makarantar furamare da ƙaramar makarantar Kuriga da ‘yan bindiga suka sace ranar Alhamis a jihar Kaduna.
Lamarin ya shafin duka duka al’ummar garin.
A yau da rana ne wani ɗalibi da ‘yan bindigar suka harba a lkacin harin ya rasu bayan kwantar da shi a asibiti sakamakon raunukan da ya ji.
Hukumomin ƙasar sun sha alwashin kuɓutar da duka ɗaliban bayan da aka jibge tarin jami’an tsaro a yankin.
Tuni dai shugaban ƙasar Bola Tinubu ya yi Allah wadai da sace ɗaliban, tare da umartar jami’an tsaro su gaggauta kubutar da su