Tashin hankali ya ɓarke a gabashin Jamhuriyar Dimukuradiyyar Congo, tsakanin jami’an tsaro da mabiya wata kungiyar addini da ke adawa da kasancewar Majalisar Dinkin Duniya a can.
Rahotanni sun ce sojoji sun kai hari kan wata tashar rediyo da kuma wani wajen bauta a birnin Goma, inda suka kashe mutum akalla tara, a yunkurin hana zanga-zangar kin jinin majalisar.
An ce, yayin dauki-ba-dadin, wani ɗan-sanda ma ya rasa ransa, inda aka yi masa atire.
Har yanzu ana cikin yanayi na dar-dar a yankin, inda shaguna da harkokin kasuwanci da dama ke rufe.
Ofishin Majalisar Dinkin Duniya a ƙasar ta Kongo na ɗaya daga cikin mafiya girma a duniya, to amma ana sukan aikinsa saboda gaza kawo ƙarshen tashin hankali tsakanin ƙungiyoyi masu makamai a gabasin ƙasar.


