fidelitybank

Sojoji Mata hudu da Hamas su ka saki sun koma Isra’ila

Date:

Sojojin Isra’ila mata hudu da Hamas ta saki sun koma Isra’ila kamar yadda rundunar sojin kasar (IDF) ta tabbatar.

Sojojin hudu wadanda su ne Daniela Gilboa, da Liri Elbag, da Naama Levy da kuma Karina Ariev, za su kasance a cibiyar da aka tanadar ta musamman wajen ajiye wadanda aka saki kafin daga bisani su gana da iyayensu.

Tun da farko kafin sakin nasu mayakan Hamas sun taru a Dandalin Falasdinu da ke Gaza, domin danka wadanda za su saki ga kungiyar agaji ta Red Cross.

Wannan shi ne kashi na biyu na Isra’ilawa da Hamas ta yi garkuwa da su da ta saki bayan cimma yarjejeniyar dakatar da bude wuta tsakaninta da Isra’ila.

Ita ma Isra’ila za ta saka wa Hamas da sakin Falasdinawa wajen 200 da take rike da su a gidajen yarinta.

Ana sa ran Hamas za ta bayar da bayani a kan wasu Isra’ilawan 26 da za ta sake saki a makonnin da ke tafe.

Sojojin Isra’ila za su janye daga muhimman wurare a Gaza, domin Falasdinawa da suka yi gudun hijira su koma arewacin birnin.

cnn news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp