Shugaban ƙasa, Bola Tinubu, ya buƙaci dakarun ƙasar da ke yaƙi da ‘yan bindiga a yankin arewa maso yammacin ƙasar, su kawo ƙarshen matsalar nan ba da jimawa ba.
Ministan tsaron ƙasar Muhammad Badaru Abubakar ne ya bayyana haka lokacin wata ziyara da ya kai shalkwatar rundunar Operation Fansar Yamma mai yaƙi da ‘yan bindigar da ke jihar Zamfara.
Badaru ya ce ”shugaban ƙasa na matuƙar damuwa da matsalar rashin tsaro da jihar zamfara ke fuskanta, kuma ya umarci sojojin ƙasar su kawo ƙarshen matalar a yankin arewa maso yammacin ƙasar baki ɗaya”.
A lokacin ziyarar ministan ya yaba da irin tsare-tsaren sojojin da ke yaƙi da ‘yan bindigar tare da umartarsu su ci gaba da farautar manyan shugannin ‘yan bindigar yankin.
Ministan ya kuma ziyarci gidan gwamnatin jihar, inda ya tattauna da gwamnan jihar kan batutuwan da suka shafi tsaro a faɗin jihar.