Matuƙan jirgin saman sojin kasar nan biyu sun tsira da rai, bayan jirgin ya yi hatsari.
Hatsarin ya faru ne a kusa da barikin sojin saman da ke Arewacin jihar Kaduna.
Rundunar sojin saman Najeriyan ta ce lamarin ya faru ne a lokacin da jirgin ke dawowa daga tuƙin koyo.
Kakakin rundunar Edward Gabkwet, ya ce “An yi sa’a duk matuƙan jirgin sun tsira da rai,”
Rundunar sojin saman ta ce an ƙaddamar da bincike kan abin da ya haddasa hatsarin.