fidelitybank

Sojoji biyu sun rasa ransu bayan fatattakar ‘yan kungiyar IS

Date:

Akalla sojoji biyu da dan sandan kwantar da tarzoma aka bayar da rahoton an kashe, bayan wani hari da ‘yan ta’addar kungiyar IS da ke Yammacin Afirka suka ka harii a wani sansanin soji a garin Molai na jihar Borno.

Al’ummar Molai na da tazarar kilomita 10 a kan titin Maiduguri zuwa Damboa, zuwa dajin Sambisa.

A cewar wata majiyar soji, ‘yan ta’addar sun kaddamar da harin ne a cikin manyan motocin yaki da dama. A cewar The Will.

Sai dai dakarun sojin Najeriya tare da na rundunar sojin sama na Operation Hadin Kai sun dakile hare-haren da aka kaddamar da Yammacin ranar Litinin da misalin karfe 6 na yamma, a kokarin da suke na fatattakar sojojin.

Sun yi artabu da sojoji na tsawon sa’a guda kafin daga bisani sojojin sama da na kasa su ka fatattaki maharan, inda aka tilasta musu ja da baya.

spw

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp