Sojoji biyu maza da wani mutum daya sun rasa rayukansu a wani hatsarin mota da ya afku a unguwar Obadeyi da ke Legas.
Hatsarin dai kamar yadda hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Legas (LASEMA) ta bayyana, ya hada da wata babbar mota da wata mota kirar Mitsubishi saloon mai lamba RNG396AA.
Rahotanni sun nunar da cewa motar na tafiya da ba daidai ba ne kuma ta yi karo da motar da mutane hudu ciki har da jami’an Soji biyu.
Sakataren dindindin na hukumar ta LASEMA, Dakta Olufemi Oke-Osanyintolu, a wani karin bayani kan lamarin, ya ce, “Abin takaici, cikin mutane hudu da ke cikin motar, sojojin Najeriya maza biyu da mace daya sun rasa rayukansu a hatsarin da ya yi sanadin mutuwarsa yayin da na karshe. Baligi namiji LASAMBUS yayi masa magani aka kaishi asibiti.