fidelitybank

Sojoji a Bama sun kama dan leken asirin Boko Haram

Date:

Dakarun runduna ta musamman ta 21 da ke Bama a jihar Borno, sun kama wani dan leken asiri na kungiyar ta’adda ta Boko Haram, Modu Babagana.

Politics Nigeria ta samu labarin cewa, Babagana ya tsere daga tsaren sojoji a Bama.
An fara kama dan ta’addan ne mai neman afuwar a watan Janairun 2020, saboda gudanar da ayyukan leken asiri kan sojoji a yankin Bama da Banki. Amma kwanaki kadan bayan an kai Babagana gidan yari, rahotanni sun ce, ya yi amfani da laya wajen saukaka tserewa daga gidan yari.

Daga bisani, hukumomi sun bayyana cewa ana neman sa.

A cikin makon nan ne aka sake kama shi tare da taimakon jami’an rundunar hadin gwiwa ta Civilian Task Force a babbar kasuwar garin Bama a lokacin da yake aikin sayan kayan aikin ‘yan ta’adda da makudan kudade.

A yayin gudanar da bincike na farko, wanda ake zargin ya amsa cewa, ya sa ido tare da bayyana inda sojojin suke da kuma motsin su ga mayakan na Boko Haram.

nigerianewspaper

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp