Dakarun Rasha sun shiga sansanin sojin saman sojojin Amurka a jamhuriyar Nijar inda har yanzu suke zaune sakamakon korarsu da sojojin da ke mulki a Nijar suka yi.
Sakataren harkokin tsaron Amurka, Lloyd Austin ya tabbatar cewa sojojin Rasha sun shiga wani sansanin sojin sama amma ɓangarensu daban.
Ya shaida wa taron manema labarai a Amurka cewa ba wata matsala ce babba ba kasancewar ba su da izinin ganin sojojin Amurka ko makamansu.
“Sansani na 101 inda sojojinmu suke, sansanin sojin saman Nijar ne da yake kusa da filin jirgin sama a babban birnin ƙasar. Ƴan Rasha na wani ɓangare daban kuma ba su da izinin shiga ɓangaren sojojin Amurka ko ma samun damar samun makamansu,” in ji shi.
Alaƙar diflomasiyya da tsaro tsakanin Amurka da Rasha ta yi tsami tun mamayar da Rasha ta yi wa Ukraine.
Kafin kifar da gwamnati a Nijar cikin shekarar da ta gabata, Amurka ta kasance babbar ƙawarta tare da sauran ƙasashe a yaƙin murƙushe masu iƙirarin jihadi a yankin.