Rundunar sojin saman kasar nan ta ce, ta fara jigilar kayan tallafin abinci zuwa birnin Maiduguri sakamakon ambaliyar da ta ɗaiɗaita mutum fiye da miliyan biyu.
Tallafin kayan abincin dai ya samu ne daga hukumar hana fasaƙauri ta Najeriya wato Customs.
Rundunar sojin saman ta ce a ranar Asabar ta fara kai kayan Maiduguri inda jiragenta suka kai shinkafa buhu 300 masu nauyin kilogram 50 kowanne, a zangon farko.
Rundunar ta kuma ƙara da cewa tuni da ma ta fara ayyukan bayar da magani ga waɗanda ba su da lafiya.