Shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky, ya ce, za su rike sojojin Rasha da suka mika wuya cikin ‘mutuntawa.
A wani jawabi da ya gabatar cikin dare Mista Zelensky ya yi kira ga dakarun Rasha da su mika wuya ga kasar Ukraine ko su san inda dare ya yi musu.
Wannan na zuwa ne bayan da shugaban Rasha Vladimir Putin ya rattaba hannu kan dokar hukunta sojojin kasar wadanda suka gudu daga fagen daga ko suka ki bin umarni, inda dokar ta tanadi daurin shekara 10 a gidan yari kan wadanda suka aikita laifin..
Kungiyar kare hakkin bil adama ta kasar Rasha OVD-Info, ta bayar da rahoton cewa an kama mutum 700 a ranar Asabar, bayan da aka tsare fiye mutum 1,000 a farkon mako.
A karkashin dokar kasar Rasha gangamin da bai samu sahalewar hukumomi ba babban laifi ne.
Yayin da yake jawabi, shugaba Zelensky na Ukraine ya umarci sojojin Rasha da su mika wuya ga Ukraine, domin kauce wa tuhumar laifin yaki bayan karewar yakin. In ji BBC.