Hukumomi a Washington sun ce wani soja ya cinna wa kansa wuta a gaban ginin ofishin jakadancin Isra’ila ranar Lahadi.
Mutumin wanda ba a tantance ba, an bayyana cewa yana cikin mawuyacin hali a asibiti.
Mai magana da yawun sojin Amurka ta tabbatar da faruwar lamarin.
Wakilin BBC ya ce wannan dai ba shi ne karon farko ba da hakan ke faruwa a bakin ofishin jakadancin Isra’ila ba a Amurka tun bayan É“arkewar yaÆ™i tsakanin Hamas da Isra’ilar.
Ko a watan Disambar bara wani ya aikata hakan a jihar Georgia.
Wani bidiyo ya É“ulla a shafukan sada zumunta inda a ciki aka ga mutum na ihu da cewa “A Æ´anta FalasÉ—inu” yayin da yake Æ™onewa, kamar yadda rahoton kafofin yaÉ—a labaran Amurka ya ce.
An tura jami’an sashen kwance bom zuwa wurin kan fargabar da aka yi game da wata mota da ake iya alaÆ™antawa da mutumin.
Daga bisani an bayyana cewa ba a gano wasu abubuwan hadari ba a cikin motar.
Ba a sami wani ma’aikacin ofishin jakadanci ba da ya ji rauni, kamar yadda mai magana da yawun ofishin jakadancin ta shaida wa jaridar New York Times.
Cikin wata sanarwa, ma’aikatar harkokin wajen Isra’ila ta ce ma’aikatan ofishin jakadancin ba su san mutumin ba.
Ƴan sanda sun ce mutumin ya yi amfani da fetur sannan an ga tutar Falasɗin a wajen da lamarin ya faru.