fidelitybank

Soji sun daƙile harin mayaƙan ISWAP a Borno

Date:

Rundunar Operation Hadin Kai wadda ke ƙarƙashin sojin Najeriya ta daƙile wani yunƙuri na harin kwanton ɓauna kan wasu motoci a kan hanyar Bama da ke Jihar Borno.

Jaridar PRNigeria ta rawaito cewa, mayaƙan ISWAP ne suka buɗe wuta a manyan hanyoyin Jihar Borno biyu. Rahotanni sun ce, tun da farko mayaƙan sun saka shingaye da dama a kwanar garin Banki, domin garkuwa da fararen hula a Ƙaramar Hukumar Bama a ranar Asabar.

Wani babban kwamanda ya shaida cewa, dakarun da ke shawagi domin tabbatar da tsaro a yankin ne suka daƙile hare-haren masu iƙirarin jihadin jim kaɗan bayan an kira su a waya an shaida musu halin da ake ciki.

Kwamandan ya bayyana cewa, mayaƙan ISWAP ɗin waɗanda suke riƙe da wasu matafiya a kan hanya, sun gudu bayan ganin sojojin, inda suka bar waɗanda suka kama.

Ya bayyana cewa, harbin bindiga da mayaƙan suka yi, ya yi sanadin fashewar gilasan baya na motocin matafiyan, amma babu wanda ya rasu.

A ɗayan ɓangaren kuma, dakarun bataliya ta 152 a yayin da suke shawagi a kan hanyar Bula Yobe – Darel Jamel a ranar dai ta Asabar sun daƙile wani harin mayaƙan na ISWAP.

Haka kuma sojojin bakwai ne, suka tsallake rijiya da baya a sakamakon nakiya da ƴan ISWAP suka dasa musu a hanyar Damboa zuwa Maiduguri.

guardian newspaper nigeria

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp