fidelitybank

Sojan Najeriya ya kashe kansa bayan an gano ɗan ƙungiyar ISWAP ne

Date:

Rahotanni daga yankin Arewa maso Gabashin na cewa wani sojan kasa, ya kashe kansa bayan da aka kama shi bisa tuhumar cewa, yana aiki tare da mayaka masu ikirari jihadi na kungiyar ISWAP.

Wakilin BBC ya ce wata majiya mai kusanci da rundunar sojojin Najeriya ta sanar da shi cewa, lallai sojan na da hannu a wasu hare-hare da aka kai kan wasu al’umomin jihar Yobe a cikin makonni da suka gabata.

Manyan hafsoshin sojin kasa sun fara sa ido kan sojan ne bayan da aka kai wasu hare-hare biyu a garuruwan Geidam da Gashua na jihar ta Yobe, kuma daga nan suka fara bibiyar wuraren da yake zuwa cikin sirri.

An kuma kama shi yayin da yake kokarin tserewa, bayan da ya gane cewa dubunsa ta cika.

Sai dai sojan wanda kwararre ne wajen sarrafa makamai, ya kwace wata bindiga a hannun daya daga cikin sojojin da ke rakiyarsa, kuma ya kashe kansa duk da cewa, an saka masa ankwa a hannu.

A makon jiya wasu wadanda ake kyautata zaton mayakan ISWAP ne suka kai wani hari kuma suka kashe akalla mutum goma, ciki har da mata.

Wannan harin ya biyo bayan wani harin na daban da aka dasa wani bam wanda ya halaka mutum shida, baya ga raunata wasu mutum 19 a jihar Taraba, harin da kungiyar ISWAP ta dauki alhakin kai shi.

vgn news 2022

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp