Slovenia ta zama ƙasar Turai ta baya-bayan nan da ta amince da ƙasar Falasdinu a hukumance, a wani mataki da gwamnatin ke fatan zai ƙara matsin lambar diflomasiyya don kawo ƙarshen yaƙin Gaza.
Wannan ƙuduri na majalisar dokokin ƙasar ya biyo bayan irin wannan mataki ne da Sifaniya da Norway da Ireland suka ɗauka a game da Falasɗinun.
Jam’iyyun hamayya sun ƙi kada ƙuri’a kan ƙudurin bayan sun kasa tilastawa a yi ƙuri’ar raba gardama kan batun.
Tsohuwar firaminista, Janez Jansha ta yi iƙirarin cewa matakin tamkar nuna goyon baya ne ga Hamas.