fidelitybank

Siyasar Kano: Kwankwaso ya aurar da diyar Shekarau

Date:

Daurin auren diyar tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Ibrahim Shekarau ya hada ‘yan siyasa daga jam’iyyu daban-daban a taron da a ka gudanar a ranar Juma’a.

A wajen taron, wanda mutane da yawa ke ganin tamkar nuna siyasa ce ba tare da dacin rai ba, tsohon gwamna, Musa Rabiu Kwankwaso ya zama Waliyyi, wanda ya baiwa Adamu Yusuf Maitama ‘yar Shekarau.

PlatinumPost ta rawaito cewa, Kwankwaso ya na da karfi a jam’iyyar adawa ta PDP yayin da Shekarau ke zaman Sanata a jam’iyyar APC mai mulki.

Daurin auren wanda ya gudana a masallacin Umar Bn Khattab da ke kan titin Zaria, ya samu halartar shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan da Sanata Barau Jibrin da dai sauransu.

Daruruwan magoya bayan manyan jam’iyyun siyasar jihar guda biyu ne su ka halarci daurin auren, kowannensu kuma na rera wakokin goyon bayan shugabanninsa, musamman ma ‘yan Kwankwasiyya da alamar jar hula ta mamaye wurin.

Yayin da Kwankwaso ya zarce gidansa bayan an daura auren, shi kuwa Shekarau ya kai shugaban majalisar dattawa zuwa gidansa, daga bisani kuma ya raka shi, domin ta’aziyyar Kwankwaso bisa rasuwar kaninsa.

A baya Shekarau ya ziyarci gidan Kwankwaso, a ranar Alhamis, domin yin ta’aziyya.

the nation newspaper 
today

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp