fidelitybank

Siyasa: Ganduje ya magantu a kan rikicin G7

Date:

Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya mayar da martani kan rikicin da ya dabaibaye jam’iyyarsa ta APC a Kano, wanda ya yi sanadiyar raba jam’iyyar zuwa gida biyu a jihar.

Da yake magana a wata hira da RFI Hausa a ranar Laraba, Ganduje ya ce fiye da shekaru 40 da ya yi a fagen siyasa, halin da Kano ke ciki yanzu ba abin damuwa ba ne.

“Halin da ake ciki a siyasa na saba gani. Kuma ko da yaushe akwai yuwuwar rarrabuwar kawuna, haka ma kuma akwai na sulhu, domin haka dukkan mu a bangarorin biyu kwararrun ‘yan siyasa ne, kuma mun yi irin wadannan abubuwan. Saboda haka jam’iyyar mu ta kasa ta dukufa wajen ganin an shawo kan rikicin, amma abin da nake kokarin bayyanawa a nan shi ne cewa, mu ba sababbi ba ne a siyasa, kuma ba kawai mun shiga ciki ba. Na shiga siyasa tun sama da shekaru 40 da suka wuce, ban da haka kuma na yi karatun siyasa a jami’a, kuma abin da mu ke yi ke nan”. Inji Ganduje.

Rikicin dai ya biyo bayan kammala taron da jam’iyyar APC ta gudanar a jihar Kano, wanda ya kai ga raba jam’iyyar gida biyu tsagin Dr Abdullahi Umar Ganduje da kuma na Malam Ibrahim Shekarau.

mmm.nnn

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp