Gwamnatin tarayya ta tabatar da cewa, an samu gurbatattun man fetur a gidajen mai a fadin tarayya.
Wannan ya biyo bayan bidiyoyin da suka yadu a kafafen sada zumunta, tun lokacin da aka ga wani gidan mai yan a matsa gurbataccen mai ga kwastoman sa.
Gwamnati ta ce ta na kokarin takaita siyar wannan gurbataccen mai na kimanin lita milyan 80.
A ta bakin hukumar lura da man fetur ta kasa NMDPR ta tabbatar da cewa, an samu matsala wajen sarrafa man feturin da aka sayarwa gidajen mai.
Hukumar NMDPR ta bayyana hakan ranar Talata inda ta ce adadi sinadarin ‘Methanol’ dake cikin feturin ya yi yawa.