Rundunar ‘yan sandan Jihar Kano, ta ce, fashewar da ta auku a wani shago a unguwar Sabon Gari a ranar Alhamis 17 ga watan Mayu, wadda ta hallaka mutum tara, ta faru ne a sanadiyyar wasu sinadarai da ake iya hada bam da su.
A lokacin da fashewar ta auku an rika yada labari masu karo da juna dangane da musabbabin abin, inda wasu ke cewa bam ne ya tashi wasu kuma ke cewa tukunyar gas ce ta mai aikin walda ta fashe a shagon.
A tattaunawarsa da wakilin BBC a wurin da fashewar ta auku, a ranar, Kwamishinan ‘yan sanda na Jihar ta Kano, CP Sama’ila Dikko, ya ce, tukunyar gas da ake walda da ita a wajen ce ta fashe, “amma ba bam ne ya tashi ba kamar yadda ake faɗa.”
A wata sanarwa da kakakin rundunar ‘yan-sandan Jihar SP Abdullahi Kiyawa, ya fitar a ranar Asabar 21 ga watan Mayu, 2022, rundunar ta ce, mutumin da yake gudanar da haramtaccen kasuwancin na sayar da wadannan haramtattun sinadarai, wadanda ake hada bam da su, da aka gano, Michael Adejo, ya mutu a fashewar.
Sanarwar ta ce, ”Binciken farko-farko ya nuna cewa daga cikin mutum tara da fashewar ta rutsa da su, daya daga cikinsu yana ajiye sinadarai masu lahani da sauran abubuwa masu hadari ba bisa ka’ida ba.
Mutum shi ne Michael Adejo, (wanda ya mutu).”
Rundunar ‘yan-sandan a wannan sanarwa ta ranar Asabar ta tabbatar da mutuwar mutum tara da kuma wasu takwas wadanda suka hada da dalibai da ta ce sun samu ‘yan raunuka a sanadiyyar fashewar ta ranar Talata.
‘Yan-sandan sun bayyana sunayen wadanda suku mutum kamar haka, Ejike Vincent (mai walda) da Michael Adejo (mai sayar da sinadarai) da Musa Kalla (mai sayar da shayi da Christiana Abosade da Mary da Austine Dada da Madam Owoleke da Omo Ben da kuma Bose Oladapo.
Rundunar ta kuma bayyana wasu tarin durum-durum da jarkoki da ke dauke da sinadarai iri daban-daban, masu hadari da ta ce ta gano a inda lamarin ya faru.