Shugabar hukumar Tarayyar Turai, Ursula von der Leyen, ta kai ziyara Ukraine, inda za ta tattauna da ƙasar kan kudirinta na shiga tarayyar.
Ms von der Leyen, ta ce, ita da Shugaba Volodymyr Zelensky za su tattauna kan batun sake gina Ukraine.
Ukraine dai na kallon shigarta ƙungiyar Tarayyar Turai a matsayin wata hanya ta ƙara inganta tsaro a ƙasar. In ji BBC.
Sai dai hukumomi da jami’ai a Turai sun ce, wannan shirin zai ɗauki shekaru ana yinsa.