Shugabar ƙasar Hungary, Katalin Novak, ta ajye aikinta saboda maganganun da suka taso bayan afuwar da ta yi wa wani mutum da aka samu da laifin alaƙa da zarafi ta hanyar lalata.
A makon da ya gabata ne shugabar ƙasar ta yi wa mutumin da aka ɗaure a gidan ayarin ƙasar afuwa, bayan kotu ta same da laifin tilasta wa ƙananan janye iƙirarin cin zarafi ta hanyar lalata da suke yi wa wani daraktan gidan kula da ƙananan yara.
Matakin afuwar ya janyo tarin zanga-zanga neman ta sauka daga muƙaminta.
Misis Novak ta nemi afuwar ‘yan ƙasar tana mai cewa ta yi ”kuskure” wajen yin afuwar.
Tsohuwar ministan shari’a Judit Varga – wadda ta sanya hannu kan takardar amincewa da afuwar – ita ta ajiye aikinta na jagorar yaƙin neman zaɓen jam’iyyar firaministan ƙasar Viktor Orban.
Ce-ce-ku-cen da ya janyo ta ajiye muƙamin nata na zuwa ne bayan da a makon da ya gabata kafar yaɗa labaran ƙasar ta wallafa sunayen mutum 25 da Misis Novak ta yi musu afuwa a watan Afrilun shekarar da ta gabata, a wani ɓangare na ziyarar Fafaroma Fransis zuwa ƙasar.
A cikin jerin sunayen ne aka ga sunan mataimakin daraktan gidan kula da ƙananan yara, da aka ɗaure shekara uku a gidan yari bayan samunsa da laifin tilasta wa ƙananan yara janye iƙirarin cewa daraktan gidan ya ci zarafinsu.