Ana sa ran wasu daga cikin shugabannin ƙasashen Afirka za su halarci jana’izar marigayi tsohon shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da za a yi yau Talata a mahaifarsa Daura.
Shugabannin ƙasashen sun haɗa da na Gambia Adama Barrow da na Chadi Mahamat Déby da na Guinea Bissau Umaro Sissoco Embaló.
Tsohon shugaban ƙasar Ghana ma Nana Akufo Addo ya yi wa iyalan marigayin ta’aziyya a Landan tun a jiya Litinin kafin gawar ta bar Landan.