Shugabannin Afirka da suka gana da shugaba Zelensky na Ukraine a jiya Juma’a, a yau Asabar kuma za su isa birnin St Petersburg domin tattaunawa da shugaba Vladimir Putin na Rasha.
Shugabannin tare da manyan jami’a daga kasashen Afirka bakwai, sun haɗa da Shugaban Afirka ta Kudu da Senegal da Zambia da Comoros.
Shugaban Afirka ta Kudu, Cyril Ramaphosa da ke jagorantar tafiyar, ya ce wannan wani yunƙuri ne na dawo da zaman lafiya ta bangaren Afirka tsakanin kasahen biyu na Ukraine da Rasha.
A birnin Kyiv, Shugaba Zelensky ya shaida musu cewa ana fa iya mayar da Rasha saniyar ware ta fuskar diflomasiyya.
Mista Putin, shi kuma a wani tsokaci daga St Petersburg a ranar Juma’a, ya ce Zelensky ya kasance abin alla-wadai ga Yahudawa.