Wata kungiyar ƙasashen yankin gabashin Afirka na shirin tura shugabanni uku zuwa ƙasar Sudan domin sasanta sojoji da ke faɗa da juna.
A ranar Lahadi ce kungiyar raya ƙasashe ta Igad ta amince da tura shugabannin ƙasashen Kenya da Sudan ta Kudu da kuma Djibouti zuwa babban birnin ƙasar Khartoum.
Har ila yau, ta yi kira da a gaggauta tsagaita wuta tsakanin ɓangarorin da ke rikici da juna a Sudan.
Sai dai da rufe filin tashi da saukar jiragen sama na kasa da kasa, babu tabbas kan lokacin da za a fara tattaunawa kan shirin zaman lafiya.
Rahotanni sun bayyana cewa ana ci gaba da gwabza fada tsakanin dakarun gwamnati da kuma dakarun kai ɗaukin gaggawa don tallafawa tsaro ta RSF, duk kuwa da rokon da ƙasashen duniya suka yi na ganin ɓangarorin da ke faɗa da juna sun tsagaita buɗe wuta.
Shugaban ƙasar Kenya William Ruto, ya bukaci shugabannin kungiyar ta ƙasashen yankin gabashin Afirka da su tashi tsaye wajen mai do da zaman lafiya a birnin Khartoum.


