Shugabanin kasashen Afrika da na gwamnatoci sama da 40 da manyan ‘yan kasuwa da dama ke halartar wani taro a birnin Washington na yaukaka dangantaka tsakanin Amurka da kasashen Afrika.
Taron na kwanaki uku da shugaban Joe Biden zai jagorenta, zai mayar da hankali ne kan dagantakar Amurka da kasashen nahiyar Afirka ta bangarori da dama.
A game da wannan taron mai tarihi, babban sakataran Amurka Antony Blinken, ya jaddada cewa wannan taro zai duba kabali da ba’adin huldodin da ke tsakanin Amurka da nahiyar Afirka.
Amurka dai ta dage haikan kai da kafa domin ta yi babban tasiri a Afirka ganin yadda China da Rasha da ma sauren kasashen duniya ke ci gaba da yunkurowa a nahiyar.
Amurka na sa ran taimaka wa kungiyar tarrayar Afirka da ta kasance mamba ta dundundun a cikin kungiyar G-20.