fidelitybank

Shugabanni sun mika saƙonnin jaje bisa mutuwar mutane 177 da jirgin sama ya fadi a Koriya

Date:

Shugabannin ƙasashen duniya sun soma aikewa da saƙonnin jaje ga gwamnatin Koriya da Kudu bisa hatsari jirgin saman da ya yi sanadin mutuwar mutane aƙalla 177.

Shugaban China, Xi Jinping na daga cikin mutanen da suka fara aikewa da ta’aziyyarsu ga iyalan mamatan.

Cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa a Telegram, Mista Xi ya ce ya kaɗu matuƙa da hatsarin jirgin.

“A madadin gwamnati da al’ummar China, ina miƙa saƙon ta’aziyya ga iyalan mutanen da suka mutu, tare da fatan samun sauƙi da waɗanda suka samu raunuka”, kamar yadda ya wallafa.

Shi ma sakataren wajen Birtaniya, David Lammy, ya ce labarin hatsarin jirgin ya tayar masa da hankali.

Cikin saƙon da ya wallafa a shafinsa na X, Mista Lammy ya jajanta wa mutanen ƙasar da na Thailand.

A baya hukumar kashe gobara ta Koriya ta Kudu ta aƙalla mutum 151 ne suka mutu a hatsarin jirgin saman ƙasar bayan da wani jirgin saman fasinja ya kauce daga titinsa yayin da yake sauka a filin jirgin sama a Koriya ta Kudu.

Hukumar kashe gobarar ta ce daga cikin wadanda suka mutu 71 maza ne, mamat 71 , yayain da suka kasa tantance jinsi gawawaki huɗu sakamakon ƙonewar da suka yi.

Jirgin dai na ɗauke da mutum 181, ciki har da ma’aikatansa shida a lokacin da hatsarin ya auku.

Jami’an agaji sun ceto ma’aikatan jirgin biyu, bayan faruwar lamarin.

Jirgin kirar Boeing 7-3-7 ya sauka, bayan dawowa gida daga Bangkok na ƙasar Thailand.

Saukar tasa ke da wuya ne ya kwace ya saki titinsa ya kutsa ta cikin wani gini, kana ya kama da wuta.

Shaidu sun ce sun ji karar fashewar wani abu mai karfi bayan faruwar lamarin. Sai dai kawo yanzu adadin ya karu.

tribune newspaper

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Zulum ya miƙa kyautar Naira miliyan 100 ga iyalan Sojojin da aka kashe

Gwamna Babagana Umara Zulum na jihar Borno, ya bai...

Otal ɗin ƴan Najeriya ya kama da wuta wani ɓangaren a Saudiyya

Hukumar Alhazai ta Najeriya ta ce an samu tashin...

An kai hari maɓoyar Boko Haram a Borno

Biyo bayan sahihan bayanan sirri da aka samu, rundunar...

Alaƙar Trump da Elon Musk ta yi tsami sosai

Attajirin da ya fi kowa arziki a duniya, Elon...

An yi jana’izar Muhammad Uwais

An gudanar da jana'izar tsohon alkalin alkalan Najeriya, mai...

Musulman Nijeriya a cigaba da jajircewa – Obi

Ɗan takarar shugaban ƙasa a karkarshin jam'iyyar Labour a...

Akwai takaici ambaliyar Neja – IBB

Tsohon shugaban ƙasa, Janar Ibrahim Babangida, ya kwatanta ambaliyar...

Farfesa Jibril Aminu ya rasu ya na da shekaru 86

Allah ya yi wa Farfesa Jibril Aminu mai shekara...

Alhajin Najeriya ya rasu a tsayuwar Arfa

Wani Alhaji daga Najeriya ya rasu a filin Arfa...

Alhazai miliyan 1.673,230 ne ke gudanar da akin Hajji – GASTAT

Hukumar tattara alƙaluma ta Saudiyya (GASTAT) ta ce, Alhazai...

Isra’ila ta gano gawar ƴan ƙasarta

Rundunar sojin Isra'ila ta ce ta gano gawar ''yan...

Ma’aikatan wutar lantarki a Abuja sun fusata

Ma'aikatar kamfanin rarraba wutar lantarki na Abuja Electricity Distribution...
X whatsapp