fidelitybank

Shugabanin ɓangarorin siyasa ku tallafawa Chadi – Buhari

Date:

Shugaban Kasa, Muhammadu Buhari, ya yi kira shugabanin ɓangarorin siyasa a Chadi da su nuna kishin ƙasa ta hanyar shiga harkokin mayar da ƙasar kan tafarkin dimokradiyya.

Yayin da yake magana da shugaban mulkin sojin ƙasar Janar Mehmet Idris Deby-Itno a wata ziyara da ya kai masa a gefe guda a taron Majalisar Dinkin Duniya da ake ci gaba da gudanarwa a birnin Doha na ƙasar Qatar ranar Lahadi.

Shugaba Buhari ya ce ”Ina ganin irin ci gaban da ake samu a ƙasarka, a matsayina na makwabci da batun ƙasarku nake kwana, kuma da shi nake tashi a zuciyata”, kamar yadda wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban Najeriya Mallam Garba Shehu ya fitar.

“Na tausaya maka, ba wai dan kana matashi ba, sai dan saboda da matsayin da wasu ƙungiyoyin da ke ƙasashen waje irinsu Libya suke ɗauka, duk da cewa wannan matsala ce da ka gaje ta daga wajen mahaifinka”, in ji Buhari

Ya kamata sauran ƙungiyoyin da ke tunanin cewa suna da ƙarfi su bayar da haɗin kai domin ceto ƙasarsu.”

Shugaba Buhari ya gode wa shugaban mulkin sojin Chadin kan ziyarar da ya kai masa tare da tabbatar masa da cewa ”a matsayinka na makwabci a shirye nake kodayaushe wajen sauraron buƙatun shawarwarinka, kan siyasa da tsaro da sauran fannoni”.

A nasa ɓangare shugaban mulkin sojin Chadin ya gode wa shugaba Buhari kan goyon bayan da yake ba shi tare da ƙasarsa a yayin da ƙasar ke shirin komawa tafarkin dimokradiyya, wanda ya ce shirin na tafiya kamar yadda ya kamata.

Ya kuma yi wa Buhari fatan alkairi tare da taya shi murnar nasarar dimokraɗiyya a Najeriya, tare da cewa ”Muna fatan ci gaba da ganinka ko bayan saukarka daga mulki”.

vanguard newspaper today

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp