Babban hafsan sojojin Sudan Laftanar-Janar Abdel Fattah al-Burhan ya kori mataimakinsa kuma kwamandan dakarun RSF Mohamed Hamdan Dagalo, wanda aka fi sani da Hemedti.
Dukkanin Janar Burhan da Hemedti sun yi aiki a matsayin shugaba da mataimakin majalisar mulkin soji, tun bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a watan Oktoban 2021.
A wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a, Janar Burhan ya naɗa tsohon madugun ‘yan tawaye Malik Agar a matsayin mataimakinsa.
Mista Agar memba ne na Majalisar mulkin sojin ƙasar.
Ya umurci sakatariyar majalisar mulki da hukumomin jihar da su gaggauta aiwatar da wannan umarni.
A watan da ya gabata ne hafsan sojojin ya rusa dakarun RSF tare da ayyana mayakan a matsayin ‘yan tawaye bayan da aka gwabza faɗa tsakanin dakarun da ke gaba da juna.
Tuni dai ƙasar ta faɗa cikin tashin hankali da ya janyo mutuwar mutane da dama da kuma raba da yawa da muhallansu.