Tsohon shugaban Afrika ta Kudu, Jacob Zuma ya tsallake ƙarin hukuncin zaman gidan yari, bayan samun yafiya.
Ana bayar da irin wannan yafiya ne ga mutanen da ba za su zama barazana ga tsaro ba.
Ministan shari’a Ronald Lamola ya shaida wa kafafen yaɗa labarai cewa an ɗauki matakin yafiyar ne domin rage cunkoso a gidajen yari. Ya ce yafiyar ta fara aiki ne daga watan Afirilu.
Zuma ya miƙa kansa ga gidan yarin Escout da ke KwaZulu-Natal da safiyar Juma’a kuma hukumomi sun karɓe shi.
Bayan sa’a guda kuma aka sake shi bisa tsarin yafiya ta musamman.
Shugaba Cyril Ramaphosa ne ya amince da yafiya ga fursunoni 9,000 waɗanda hukumomi suka tabbatar ba su da barazana ga tsaron ƙasa.
A watan Yunin 2021 aka yanke wa Zuma hukuncin zaman gidan yari na wata 15, bayan kama shi da laifin ƙin amsa gayyatar kotun da ke binciken zamanin mulkin sa.
Daga baya aka sallame shi daga gidan yarin domin ya samu damar ganin likita, bayan an tsare shi na tsawon wata biyu.