Shugaban kasar Ukraine Volodymyr Zelensky ya kai ziyara Bucha, a yayin da ake samun karin shaidu kan ta’asar da aka yi a kusa da Kyiv.
Ya zagaya kan hanyar da aka yi wa dakarun Rasha kwanton-bauna kuma ya yi magana da mutanen yankin.
Ya jaddada ikirarin da ya yi cewa, Rasha ta aikata laifukan yaki da kuma kisan kare-dangi a Ukraine.
Da BBC ta tambaye shi kan ko akwai yiwuwar tattaunawar zaman lafiya tsakaninsu da Rasha, sai ya ce: “Eh, saboda dole Ukraine ta samu zaman lafiya. Muna Turai a karni na 21. Za mu ci gaba da yunkurin difilomasiyya da soja.”