fidelitybank

Shugaban Turkiyya ya nemi ƴan ƙasarsa su fito su marawa Falasɗinawa baya

Date:

Shugaban Turkiyya Recep tayyip Erdogan, ya yi tir da hare-haren da Isra’ila ta kai cikin dare a Gaza waɗanda ya ce sun “ƙara ta’azzara halin da ake ciki”.

Cikin wani saƙo da ya wallafa a dandalin X, wanda aka sani a baya da Twitter, shugaban ya nemi ‘yan ƙasarsa su fito zanga-zangar nuna goyon baya ga Falasɗinawa.

“A yau, ina gayyatar ‘yan uwana zuwa babban maci don Falasɗinawa a Filin Jirgin Sama na Ataturk, Istanbul, inda za mu nuna goyon bayan Falasɗinawa da babbar murya a hare-haren da Isra’ila ke kai musu,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa “dole ne Isra’ila ta koma cikin hankalinta kuma ta dakatar da waɗannan hare-hare”.

Da ma tuni dubban ‘yan Tukriyya suka dinga nuna goyon bayansu ga Falasɗinawan duk ranar Juma’a tun daga fara yaƙin a ranar 7 ga watan Oktoba.

Zuwa yanzu, Isra’ila ta kashe mutum fiye da 7,000 a Zirin Gaza da Gaɓar Yamma da Kogin Jordan da ta mamaye, a cewar ma’aikatar lafiya ta Falasɗinawa.

Isra’ilar na cewa tana kai harin ramuwar gayya ne bayan mayaƙan Hamas sun tsallaka iyaka tare da kashe mutum 1,400 a ƙasar.

legit

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp