fidelitybank

Shugaban Sojojin Isra’ila ya yi murabus dalilin kai hari da Hamas ta yi

Date:

Shugaban sojin Isra’ila ya yi murabus daga mukaminsa, saboda abin da ya kira gazawarsa a harin ranar 7 ga watan Oktoba da Hamas ta kai cikin kasar, wanda kuma shi ne sanadiyyar yakin Gaza.

Cikin wata wasika da ya aike wa ministan tsaron kasar, Laftnar Janar Herzi Halevi ya amince cewa rundunar sojin Isra’ila, IDF, ta ”Gaza aiwatar da hakkin da ya rataya a kanta na kare ‘yan Isra’ila”

“Gazawata da ta janyo wannan mummunan abu a kullum yana ta bibiyata, kuma zan ci gaba da nadama har karshen rayuwata,” in ji shi.

Jim kadan bayan aika wasikar tasa, sai shugaban rundunar IDF mai kula da yankin kudancin kasar, Manjo Janar Yaron Finkelman, shi ma ya ayyana sauka daga mukaminsa, yana mai cewa shi ma ya gaza a hakkin da ya rataya a kansa na kare yammacin Negev da al’ummar yankin.

Saukar jagororin IDF din na zuwa ne kwana uku bayan fara aiwatar da yarjejeniyar tsagaita wuta da fara sakin Isra’ilawan da Hamas ta yi garkuwa da su a lokacin harin ranar 7 ga watan Oktoban 2023.

www.nigeriannewspapers.com

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp